in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalissar kolin Sudan ta sha alwashin hukunta wadanda suka hallaka masu zanga zanga
2019-04-12 19:25:04 cri
Majalissar kolin soji dake mulkin wucin gadi a kasar Sudan, ta sha alwashin hukunta wadanda suka hallaka masu zanga zanga a kasar. Shugaban kwamitin siyasa na majalissar Omer Zainal-Abdin ne ya bayyana hakan, biyowa bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a jiya Alhamis.

Zainal-Abdin ya kuma bayyana aniyar majalissar, game da yiwuwar rage wa'adin aikin majalissar daga shekaru biyu zuwa kasa da hakan. Kaza lika Mr. Zainal-Abdin ya ce ba za a mika tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir ga kotun kasa da kasa ta hukunta manyan laifuka ko ICC ba. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China