in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin jihar Borno ta gina makarantu ga marayun da suka rasa iyayensu sanadiyyar ayyukan Boko Haram
2019-04-13 15:54:02 cri
Gwamnatin jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya, ta kammala ginin manyan makarantun zamani 45, domin bada ilimi kyauta ga marayun da suka rasa iyayensu sanadiyyar ayyukan kungiyar Boko Haram.

Wata sanarwar da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Alhamis a Abuja, babban birnin Nijeriya, ta ce ginin makarantun wani bangare ne na manufar inganta samar da ingantaccen ilimi ga marayu da yaran da suka daina zuwa makaranta.

Kiddidigar gwamnatin jihar ta ce, sama da yara 53,000 ne suka zama marayu, yayin da mata 50,000 suka rasa mazajensu, sanadiyyar ayyukan Boko Haram da aka fara a jihar tun a shekarar 2009.

An gina sabbin makarantun ne a yankunan kananan hukumomin jihar 27, inda suka kunshi kayayyakin koyo ta na'urori da janareto da na'urorin AC mai sanyaya yanayi da kuma sauran kayayyakin karatu na zamani. Za a dauki dalibai ne daga fadin yankunan kananan hukumomin jihar.

Makarantun sun hada da makarantun firamare da na karamar sakandare 42 da wasu karin gine-ginen 13 domin tabbatar da an fadada aikin samar da ilimi.

Bugu da kari, sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta fara gangamin karfafa gwiwar mayar da yaran da suka daina karatu, makaranta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China