in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata arangama tsakanin 'yan sinitiri da 'yan bindiga ta yi sanadin mutuwar mutane 7 a Nijeriya
2019-04-10 09:35:37 cri

Wata arangama tsakanin 'yan kungiyar sintiri da wasu 'yan bindiga a jihar Katsina dake arewa maso yammacin Nijeriya, ta yi sanadin mutuwar mutane 7.

Rundunar 'yan sanda jihar ta ce ta gano gawawwaki 7 jiya da safe, biyo bayan arangamar da aka yi ranar Litinin, wadanda ake tsammanin na mambobin kungiyar sintiri ne, na kauyen Tsamiyar Jino dake karamar hukumar Kankara ta jihar.

Kakakin rundunar Gambo Isa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, da jin labarin wasu 'yan bindiga na taruwa a wani daji dake kusa da kauyen, sai 'yan sintirin suka kai musu farmaki ba tare da tuntubar rundunar 'yan sandan ba.

A cewar mazauna kauyen, 'yan bindigan sun shafe wani lokaci suna addabar yankin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China