Babban Sufeton 'yan sandan kasar Muhammad Adamu, ya bayyanawa manema labarai jiya a Abuja cewa, gwamnatin ta kuma umarci dukkan 'yan kasashen waje dake ayyukan hakar ma'adinai su bar yankin cikin sa'o'i 48.
Ya ce umarnin wani bangare ne na matakan dakile ayyukan bata gari a jihar.
A cewar Babban Sufeton, dakatarwar ta biyo bayan rahotannin sirri da aka samu cewa, akwai alaka mai karfi tsakanin ayyukan bata garin da masu hakar ma'adinai bisa haramtacciyar hanya. (Fa'iza Mustapha)