in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da samun sabbin rahotannin bullar cutar zazzabin Lassa 16 a Najeriya
2019-04-07 15:27:24 cri
A ranar Asabar hukumomin lafiya a Najeriya sun tabbatar da samun sabbin rahotannin bullar cutar zazzabin Lassa a makon da ya gabata a jahohi 5 na kasar ta yammacin Afrika.

Samun sabbin rahotannin na baya bayan nan ya tabbatar da jimillar rahotannin bullar cutar 526 daga cikin adadin da ake zargi na kimanin 2,034 tun daga watan Janairu a jahohin kasar 21, Chikwe Ihekweazu, babban jami'in hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriya (NCDC) shi ne ya bayyana hakan a Abuja, babban birnin Najeriyar.

Ya shedawa manema labarai cewa, adadin mutane da suka mutu sun kai 121 tun bayan barkewar annobar cutar.

Ihekweazu ya kara da cewa akwai wasu jami'an kiwon lafiya cikin wadanda lamarin ya rutsa da su a jihar Filato dake shiyyar tsakiyar Najeriya, inda kawo yanzu aka samu ma'aikatan jiyya 17 da cutar ta shafa a jahohi 7 na kasar tun bayan barkewar cutar.

Shugaban hukumar ta NCDC ya tabbatar da cewa, manyan abokan aikin hukumar na kasa dake yaki da cutar ta Lassa, da manyan cibiyoyin ba da agajin gaggawa za su ci gaba da yin aiki tare domin dakile cutar a dukkanin matakai. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China