Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta tabbatar da mutane 21 sun mutu a wani hari da wasu, da ba a san ko su waye ba, suka kai jihar Kaduna dake arewacin kasar.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo, ya shaidawa manema labarai cewa, wasu 'yan bindiga sun kai hare-hare kauyukan Ungwan Aku da Banono na yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar.
Yakubu Sabo ya ce an gano gawawwaki 21, sannan wasu mutane 3 sun ji rauni, baya ga kone gidaje 10 da maharan suka yi.
Duk da barnar da suka yi a kauyukan, 'yan bindigan sun kuma sace shanu 50 yayin harin.
Kakakin 'yan sandan ya ce 'yan bindigar sun kai farmaki kauyukan ne a kan babura.
Ya kara da cewa, tuni aka kaddamar da bincike kan lamarin. (Fa'iza Mustapha)