in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin EEC na kasar Sin ya fara aikin gina wata hanya a jihar Gomben Najeria
2019-04-05 15:30:22 cri

A jiya ne kamfanin EEC na kasar Sin ya fara aikin gina wata hanya da za ta kawo gajiya a yankunan karkarar jihar Gombe dake yankin arewa maso gabashin kasar, da nufin bunkasa tattalin arzikin yankunan.

Aikin gina hanyar da kamfanin na EEC ke gudanarwa, wani bangare na kamfanin CRCC, ana saran idan an kammala ta, za ta samarwa al'ummomi uku dake karamar hukumar Yamaltu/Deba da hanyoyin zirga-zirga. Hanyar mai nisan kilomita 9, da ta hade al'ummomin manona uku dake yankin, da suka hada da Boltongo, Non da kuma Deba, za a kammala ta ne cikin watanni 15.

Da yake karin haske Sarkin Deba, Ahmad Usman, ya ce, karin al'ummomin dake kusa da yankin za su ci gajiyar aikin hanyar, za kuma ta bunkasa tattalin arziki da ma kawo ci gaba a yankin.

Kafin fara aikin hanyar, kananan manoma na fuskantar babban kalubale na jigilar kayan amfanin gonakinsu zuwa birane. Kana a lokutan damina, yanayin na kara tsanani, inda suke fuskantar matsalar zirga-zirgar a hanyar mai cike da tabo.

Ya ce, hanyar za ta saukakawa jama'a, tare da kawo karshen kuncin da suka dade suna fama da ita.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China