in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cinikayyar tsakanin jihar Tibet ta kasar Sin da kasashen ketare ya yi karfi a 2018
2019-02-18 16:32:32 cri
Cinikayya tsakanin kasashen ketare na jihar Tibet mai cin gashin kanta dake kudu maso yammacin kasar Sin, ta tsaya da kafarta a shekarar 2018.

Bayanai a hukumance sun nuna cewa, darajar kayayyakin da aka shigar da wadanda aka fitar daga jihar a bara, ta kai yuan biliyan 4.752 kwatankwacin dala miliyan 701. Sannan cinikayya tsakanin mazauna iyakar jihar ta zarce yuan miliyan 100, wanda ya karu kan na shekarar 2017 da kaso 169.3. Cinikayya tsakanin jihar da Nepal kuwa, ta kai kaso 4.6, wanda ya mamaye kaso 52.6 na jimilar cinikayyar da jihar ta yi da kasashen ketare.

Tibet ta fitar da jerin matakan inganta cinikayya a kan iyaka, yayin da kuma ta shiga ana damawa da ita cikin shawarar ziri daya da hanya daya, wanda ya bada gagarumar gudunmuwa ga ci gaban cinikayyarta da kasashen waje.

A cewar Liu Dali, shugaban hukumar Custom na Lhasa, babban birnin jihar, hukumomin jihar masu inganta dangantakar tattalin arziki da kasashen kudu maso yammacin da kudu maso gabashin Asiya, su ma sun bada gudumuwa ga tsayuwar tattalin arzikin da kafarta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China