in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban rikon kwarya na kasar Aljeriya ya lashi takobin shirya zabe cikin watanni 3
2019-04-10 17:01:20 cri

Shugaban rikon kwarya na kasar Aljeriya, Adelkader Bensalah, ya ce babban abun da zai sa a gaba shi ne, shawo kan takkadamar siyasar kasar domin samun damar gudanar da zaben sabon shugaban kasa nan ba da dadewa ba.

A cikin jawabinsa na farko da kafofin yada labarai na kasar suka watsa, Adelkader Bensala, ya jinjinawa al'umma da jami'an tsaron kasar da suka gudanar da harkokinsu bisa kwarewa, kuma yadda ya kamata, yayin boren da aka fara a fadin kasar ranar 22 ga watan Fabrairu, la'akari da cewa kawo yanzu, babu wani babban rikici da ya auku.

Ya bayyana yanayin da ake ciki yanzu a matsayin mai muhimmanci ga tarihin kasar, yana mai jaddada cewa, babban abun da zai sanya gaba shi ne, tabbatar da mika mulki ga zababben shugaban kasar cikin watanni 3, bayan gudanar da sahihin zabe bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasar.

Shugaban na rikon kwarya ya kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su yi aiki tare, wajen samar da dokokin da za su kafa hukuma mai zaman kanta, da za ta shirya zaben.

Ya karkare da yin kira ga al'ummar kasar su kwantar da hankalinsu gabanin zaben sabon shugaban kasa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China