in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Afrika 52 ne aka ceto a gabar ruwan Aljeriya
2019-01-28 09:51:23 cri

Dakarun rundunar sojin ruwan Aljeriya, sun ceto bakin haure 'yan Afrika 52 a yammacin yankin Ghazaouet dake lardin Tlemcen na kasar.

Gidan talabijin na kasar ENTV, ya bayyana cewa, kwale-kwalen bakin hauren 52 da suka fito daga kasashen Afrika daban daban, ya karye ne lokacin da aka samu guguwa a yankin arewacin kasar, sai dai dakarun dake sintiri a yankin sun yi nasarar cetonsu a kan lokaci.

Majiyar ta kara da cewa, an samu 7 daga cikin bakin hauren cikin mawuyacin yanayi, inda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.

Bakin hauren dai na kokarin zuwa kasar Spaniya ne la'akari da cewa tekun Aljeriya na kusa da zirin Iberia.

Har ila yau, majiyar ta ce hukumomin za su kula da mutanen, sannan za a mayar da su kasashensu na asali. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China