in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Algeria Bouteflika ya janye daga takarar neman shugabancin kasar
2019-03-12 10:13:05 cri

Shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika, ya sanar a jiya Litinin cewa ya janye aniyarsa ta neman sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa, kamfanin dillancin labaran kasar APS ne ya bada rahoton.

A wani sakon da ya aikewa 'yan kasar, Bouteflika ya ce, ba zai sake neman wa'adin shugabancin kasar a karo na biyar ba, sanarwar ta ce, zaben shugabancin kasar wanda aka shirya gudanarwa a ranar 18 ga watan Afrilu an dage shi zuwa wani lokacin da ba'a bayyana ba.

Bouteflika ya ce, matakin janye takarar tasa ya biyo bayan ci gaba da zanga zangar da ake ci gaba da gudanarwa ne a duk fadin kasar.

Za'a sanar da takamammiyar ranar zaben shugaban kasar ne a lokacin babban taron kasar da za'a gudanar, kana za'a gudanar da zaben ne karkashin kulawar sabuwar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar wanda wasu manyan jami'ai masu zaman kansu za su jagoranci hukumar, in ji Bouteflika.

Miliyoyin 'yan kasar Algeria ne ke ci gaba da yin zanga zanga tun a ranar 22 ga watan Fabrairu domin yin matsin lamba ga shugaban kasar mai shekaru 82 da ya janye aniyarsa ta neman sake tsayawa takarar shugabancin kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China