in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Aljeriya ta nada Abdelkader Bensalah a matsayin shugaban kasar na rikon kwarya
2019-04-10 11:23:35 cri

Majalisar dokokin Aljeriya ta nada Abdelkader Bensalah a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya a jiya Talata, bayan murabus da shugaba Abdelaziz Bouteflika ya yi a makon jiya.

A cewar gidan talabijin na ENTV na kasar, mambobin majalisar 453 daga cikin 487 ne suka kada kuri'ar ayyana kujerar shugaban kasar a matsayin wanda babu kowa, tare kuma da nada Shugaban majalisar dattawan kasar a matsayin shugaba na rikon kwarya na watanni 3, kafin a yi sabon zaben shugaban kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

An nada Abdelkader Bensalah a matsayin shugaba na riko ne yayin zaman hadaka na majalisun dokokin kasar biyu, yayin da mambobin jam'iyyar adawa da na indipenda suka kauracewa zaman.

Bayan nadin, Adelkader Bensalah, ya sha alwashin kiyaye kundin tsarin mulkin kasar, inda ya ce zai yi aiki wajen ba al'ummar kasar 'yancin zaben sabon shugaban kasa bisa tsarin demokradiyya, yana mai cewa, Aljeriya ta shiga wani sabon zamani.

Yayin da zaman majalisun ke gudana ne kuma dalibai a Tripoli babban birnin kasar, da wasu larduna da dama, suka fantsama kan tituna, domin nuna rashin amincewarsu da nadin Bensalah.

Abdelaziz Bouteflika ya yi murabus ne a ranar 2 ga watan nan, biyo bayan boren da dubban jama'a a fadin kasar suka fara tun ranar 22 ga watan Fabrairu, suna neman shugaban ya sauka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China