Sanarwar ta ce, shugaba Bouteflika zai yi murabus kafin ranar 28 ga watan Afrilu, wanda ita ce ranar da wa'adin mulkinsa zai kare.
Wata majiya ta bayyana cewa, Bouteflika zai dauki wannan muhimmin mataki ne bisa tsarin dokar kundin tsarin mulkin kasar, domin tabbatar da ganin ma'aikatu da hukumomin gwamnatin kasar suna ci gaba da tafiyar da al'amurransu yadda ya kamata a lokacin da za'a gudanar sauyin shugabanci a kasar wanda zai fara tun daga ranar da shugaban ya yi murabus.
A daren ranar Lahadi, shugaba Bouteflika ya nada sabbin mambobin hukumar zartaswar kasar wanda firaiministan kasar Noureddine Bedoui ke jagoranta. Makasudin kafa sabuwar majalisar ministocin shi ne, domin tabbatar da ganin an tafiyar da sauyin shugabancin kasar cikin kwanciyar hankali. (Ahmad Fagam)