Kiraye-kirayen da hukumar zaben kasar ta yi inda ta bukaci masu kada kuri'u a zaben shugaban kasar dake tafe, wata alama ce dake tabbatar da cewa kasar Algeria tana yunkurin tabbatar da daya daga cikin muhimman matakan kasa da kasa na samar da shugabanci na gari, Abdulwahab Dirbal, babban jami'in hukumar zaben kasar shi ne ya bayyana hakan ta kafar gidan radiyon kasar.
Tun da farko, Ali Ghediri, tsohon daraktan ma'aikatar tsaron kasar ya sanar da cewa, zai tsaya takarar neman shugabancin kasar a zaben shugaban kasar da za'a gudanar ranar 18 ga watan Afrilu.
Ghediri, mai shekaru 64 a duniya, shi ne mutum na farko da ya bayyana aniyarsa ta neman karawa da shugaban kasar mai ci Abdelaziz Bouteflika, dan shekaru 81 a duniya, wanda ya dare shugabancin kasar tun a shekarar 1999.
A bisa dokar kundin tsarin mulkin kasar, wajibi ne 'yan takarar dake neman shugabancin kasar su yi rajista da kotun tsarin mulki ta kasar kafin ranar 4 ga watan Maris.
Rashin tabbas dangane da ko Bouteflika zai sake tsayawa takarar neman shugabancin kasar ya haifar da rudani a fagen siyasar kasar ta Algerian cikin watannin da suka gabata. (Ahmad Fagam)