in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci gwamnatocin Afrika su samar da shiri mai dorewa na inganta rayuwar yara da matasa
2018-11-03 16:57:37 cri

Wani sabon rahoto ya bayyana karuwar adadin yara da matasa a nahiyar Afrika a matsayin babban kalubale, sai dai a wani bangare, za a iya amfani da ita a matsayin kyakkyawar dama.

Rahoton mai taken "yanayin rayuwar yara na 2018: nasarar gwamnatoci wajen inganta rayuwar yara", wanda aka wallafa jiya a birnin Addis Ababa na Habasha, ya yi gargadin cewa, nahiyar Afrika ka iya zama mattatarar fusatattun yara da matasa da ba sa samun isasshen abinci da ilimi da aikin yi ya zuwa shekarar 2050.

Rahoton ya bukaci gwamnatocin Afrika su himmantu wajen samar da dawwamammen shirye-shiryen samar da abinci mai gina jiki da kiwon lafiya da ilimin yara da matasa, domin kaucewa shiga wancan hadari.

Assefa Bequele, daraktan zartarwa na dandalin tsara manufofin kyautata rayuwar yaran Afrika, wanda ya hada rahoton, ya ce nahiyar Afrika za ta iya zabar samun ci gaban tattalin arziki daga yawan al'umma masu jinni a jika, da amfana daga yawan al'ummarta, da kuma gaggauta samun ci gaba mai dorewa.

Ya ce, yara na da damar da za su iya sauya nahiyar, amma idan aka yi watsi da su, za su ta'azzara wahalar da ake sha ta talauci da rashin daidaito, tare da yin barazana mai tsanani ga tsaro da zaman lafiya da ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China