in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF: Yaran Nijeriya sama da miliyan 10 ba su samu damar shiga makaranta ba
2018-11-21 10:34:24 cri
Asusun kula da yara na MDD (UNICEF) a jiya Talata ya bayyana cewa, yara kanana sama da miliyan 10 a tarayyar Najeriya ba su samu damar shiga makaranta ba.

Wakilin asusun na UNICEF a Najeriya Mohamed Fall, ya bayyana hakan ne a Abuja fadar mulkin kasar, cewa Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a fannonin kiwon lafiyar yara, da rage mutuwar jarirai da yara masu shekaru kasa da biyar, a sakamakon cutar malariya.

Wakilin ya kara da cewa, ana ci gaba da fuskantar kalubale wajen aiwatar da yarjejeniyar kare hakkin yara da gwamnatin Nijeriya ta amince da ita, musamman ta fannonin raba albarkatun da ake da su, da kuma aiwatar da abubuwan da suka shafi yara.

Wakilin ya kara da cewa, a sakamakon yadda aka inganta tsaftar muhalli da ta jiki, an samu raguwar mutuwar yara masu shekaru kasa da biyar, kuma karin yara na samun damar zuwa makaranta.

Wakilin ya kuma bukaci hukumomi na matakai daban daban, da sassa masu zaman kansu, da al'ummomin kasar, da su hada kansu don daidaita wadannan matsalolin da ake fuskanta. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China