in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nahiyar Afrika ta kaddamar da gangamin magance batun yaran dake watangarari a titi
2018-11-25 16:02:59 cri
Biranen Afrika, sun kaddamar da wani gangami jiya a birnin Marrakech na Morocco, da nufin magance karuwar matsalar watangararin yara a titi a nahiyar.

Kungiyar birane da kananan hukumomin nahiyar Afrika (ULCG Africa) ce ta kaddamar da gangamin mai taken "Biranen Afrika da babu yara kan tituna" da hadin gwiwar hukumar kare hakkin yara ta Morocco.

An sanar da gangamin ne, a wani bangare na taron biranen Afrika karo na 8 da ya gudana a Marrakech daga ranar 20 zuwa 24 ga watan nan.

Manufar gangamin ita ce, jan hankalin kowa da kowa, domin nuna adawa da yadda karin yara da ya kamata a ce suna tare da iyalansu a gida ko kuma sun makaranta, ke watangarari a titunan biranen Afrika, inda za su iya saukin fadawa cikin hadari.

An gabatar da gangamin ne la'akari da yadda matsalar yara da ke garari a titi ke zama daya daga cikin matsalolin al'umma a biranen Afrika.

A cewar mashirya gangamin, sama da yara miliyan 30 ne ke fafutukar rayuwa a Afrika, adadin da ya dauki 1 bisa 4n yara miliyan 120 dake watangarari a duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China