in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka na fatan samar da tsare tsare na kare yara dake gabashi da kudancin nahiyar
2019-01-22 20:32:03 cri

A karon farko a tarihi, sassan masu rajin kare hakkokin yara daga kasashen nahiyar Afirka 27, za su gudanar da wani taro a birnin Windhoek na kasar Namibia, da nufin tattauna kalubale da yara ke fuskanta, da hanyoyin raya ci gaban su, da nufin samar da wani tsari managarci, na kare 'yancin yaran dake gabashi da kudancin nahiyar.

Za a gudanar da taron ne dai a ranar 11 ga watan Fabarairun dake tafe, ana kuma sa ran halartar wakilai daga kungiyar SOS International dake Austria, da na ofishin yanki, na kula da hakkokin yaran yankin gabashi da kudancin Afirka ko ESAF a takaice.

Da take tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Talatar nan, manajar hukumar kasar Namibia mai kare hakkin yara Christine Esperanza Aochamus, ta ce yankin na fama da matsaloli masu alaka da keta hakkokin yara, wadanda kawo yanzu ba a kai ga shawo kan su ba tukuna. Kaza lika da yawa daga masu aikata irin wadannan laifuka na watayawar su, ba tare da an dauki matakin shari'a a kan su ba duk kuwa da a mafi yawancin lokuta ana gabatar da korafi ga mahukunta.

Jami'ar ta kara da cewa, ana fatan taron zai samar da wata dama, ta fadakar da al'umma game da wadannan batutuwa, da fatan samar da karin kafofin wayar da kai da za a aiwatar bayan kammala taron.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China