in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci Afrika su kawar da dabi'ar cin zarafin yara ta jefa su yin latata ta hanyar intanet
2019-03-07 10:50:28 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta yi kira ga kasashen Afrika da su kawar da barazanar jefa kananan yara yin lalata ta hanyar shafukan intanet.

AU ta yi wannan kiran ne a matsayin na gaggawa a yayin da ta fara wani taron tuntuba a tsakanin nahiyar game da yadda za'a kawar da jefa rayuwar kananan yara cikin aikata lalata ta hanyar shafukan intanet wato (OCSE) a takaice, shirin wanda ke guda daga ranar 6 zuwa 8 ga watan Maris a hedkwatar kungiyar ta AU dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Kungiyar Au ta ba da sanarwar cewa, "amfani da shafukan intanet a Afrika ya yi matukar karuwa a cikin 'yan shekarun nan. Yayin da ake samun bunkasuwar tattalin arziki da kyautata yanayin zamantakewa, a hannu guda kuma, akwai barazanar jefa kananan yara cikin hali na aikata latata ta hanyar shafukan na intanet."

Kungiyar mai mambobin kasashe 55 daga fadin nahiyar ta Afrika, tana cigaba da aikin wayar da kai domin kawar da barazanar jefa rayuwar kananan yara cikin hadin hadarin yin lalata, kana ta bayyana wannan barazanar a matsayin aikata babban laifi ta shafukan intanet dake bukatar dakile shi cikin gaggawa.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, taron, ya kunshi wasu manyan jami'an hukumomin samar da dokokin kare hakkin kananan yara daga dukkan kasashen mambobin AU, ana saran taron zai sa kaimi wajen zaburar da jami'an siyasa da shugabannin kasashen wajen shawo kan matsalolin bayan irin nasarorin da ake sa ran samu a taron.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China