in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana'antar Nollywood na maraba da masu zuba jari daga ketare
2019-04-03 12:46:54 cri
Masu ruwa da tsaki a masana'antar shirya fina finai ta kudancin Najeriya ko Nollywood a takaice, sun bayyana kudurinsu na karbar masu zuba jari daga kasashen ketare, ta yadda hakan zai taimakawa ci gaban masana'antar.

Yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, daya daga kungiyar taurarin masana'antar Segun Arinze, ya ce Nollywood na kan gaba a duniya wajen samar da fina finai masu kayatarwa, musamman idan aka yi duba da yawan fina finai da masana'antar ke fitarwa a duk mako. To sai dai kuma a cewarsa, batun samun isassun kudade na zama wani babban kalubale, don haka suke fatan samun jari daga masu sha'awar wannan sana'a tasu daga ketare.

Arinze ya kara da cewa, fina finai da ake hadawa a Najeriya sun fara karade tashoshin talabijin na sassan nahiyar Afirka, da ma wasu sassan kasashen duniya tun daga farkon shekarun 2000. A daya hannun kuma, masoya kallon fina finan na Nollywood a kasashen waje, na ci gaba da karuwa musamman ma a kasar Birtaniya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China