in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani gini mai hawa 3 ya rushe a garin Ibadan na Nijeriya
2019-03-16 15:28:20 cri

Wani gini mai hawa 3 ya rushe a garin Ibadan dake kudu maso gabashin Nijeriya, inda ake fargabar ya rufta da wasu mutane.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Oyo, Shina Olukolu, ya ce ginin da ba a kammala aikinsa ba ya ruguje ne a wata unguwa mazaunar jama'a, dake birnin Ibadan na jihar Oyo.

Shina Olukolu, ya tabbatar da cewa kawo yanzu, an ceto mutane 3.

Mazauna unguwar sun ce, galibin wadanda lamarin ya rutsa da su laborori ne dake aikin ginin. Wasu daga cikin mazaunan sun yi dandazo a wurin domin kokarin ceton wadanda suka makale karkashin baraguzan ginin.

Wannan lamarin ya auku ne kwanaki 2 bayan makamancin ginin ya rushe a birnin Lagos, inda ya yi sanadin mutuwar mutane 20, ciki har da yara 'yan makaranta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China