in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu fashin banki sun kashe mutane a kalla 7 a Najeriya
2019-04-09 10:14:17 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla mutane 7 ne suka gamu da ajalinsu, sakamakon wani hari da 'yan fashi suka kai a wani bankin kasuwanci a jihar Ondo dake kudu maso yammacin kasar.

Wani ganau ya bayyana cewa, 'yan fashin dauke da makamai, sun farma bankin ne a yammacin jiya, inda suka rika ihu suna harbin kan mai uwa da wabi, suka kuma kashe mutane a kalla 7, ciki har da jami'an bankin da kwastomomi da wani dan sanda. 'Yan fashin sun kuma yi awon gaba da makuden kudade kafin isowar jami'an tsaro.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Femi Joseph, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua aukuwar lamarin ta wayar tarho, sai dai, bai yi wani karin haske kan lamarin ba.

Wani shugaban al'umma mai suna Olatunji Oshati, ya bayyana lamarin a matsayin mai tayar da hankali. Ya kuma jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, inda ya kuma bukaci hukumomin da abin ya shafa, da su kara tsaurara matakan tsaro a yankin Idoani da kewaye.

Wasu rahotanni na cewa, 'yan fashin sun shigo harabar bankin ne cikin wata motar kawa, inda suka kutsa kai cikin bankin, bayan da suka yi amfani da abubuwan fashewa wajen tarwatsa kofofin tsaron bankin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China