in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya na shirin kafa asusun kula da masu zazzabin lassa
2019-04-09 09:18:45 cri

Hukumomin lafiya a Nijeriya, sun ce nan ba da dadewa ba, kasar za ta kaddamar da asusun kula da lafiya domin kula da wadanda aka tabbatar sun kamu da zazzabin lassa da kuma tabbatar da kudi bai kawo cikas wajen samun kulawar lafiya ba.

Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da hukumar takaita yaduwar cututtuka ta kasar NCDC ta fitar jiya a Abuja, inda ta ce batun shi ne abun da aka mayar da hankali kansa, a dukkan matakan gwamnatin kasar a yanzu.

Shugaban hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu, ya ce suna shirye-shirye ta asusun kula da lafiya a matakin farko, sabon asusun da gwamnatin kasar ta kafa, domin biyan kudin kula da wadanda aka tabbatar suna fama da zazzabin lassa.

Manufar asusun ita ce, tabbatar da biyan kudin bai zama matsalar da za ta hana samun kulawar cututtukan dake kama al'umma kamar zazzabin lassa.

Ya ce kafin kaddamar da asusun, gwamnatin na aiki domin ragewa marasa lafiya matsin samun kulawar zazzabin lassa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China