in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya aike da wasikar taya murnar kafa cibiyar nazarin Afirka ta kasar Sin
2019-04-09 13:44:00 cri

A yau Talata ne, aka gudanar da taron kafa cibiyar nazarin Afirka ta kasar Sin a nan birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murnar kafa cibiyar.

A cikin wasikar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a karkashin sabon yanayi, an kara sada zumunta tsakanin Sin da Afirka, da kara yin hadin gwiwa da juna, da yin mu'amalar al'adu da juna, wanda ya amfanawa jama'ar Sin da Afirka, kana ya samar da gudummawa wajen raya sha'anin kiyaye zaman lafiya da samun ci gaba a duniya.

Xi Jinping ya bayyana cewa, a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a shekarar 2018, Sin da Afirka sun tsaida kudurin cimma buri iri daya na Sin da Afirka, da aiwatar da shirye-shirye 8 na raya hadin gwiwar dake tsakaninsu. Kafa cibiyar nazarin Afirka, muhimmin mataki ne na kara yin mu'amalar al'adu da juna. Yana fatan za a yi amfani da albarkatun masana kan harkokin Sin da Afirka dake cikin cibiyar wajen kara fahimtar juna da sada zumunta a tsakanin jama'ar Sin da Afirka, yana mai cewa ta haka za a samar da shawarwari da bada ra'ayoyi kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da sauran bangarori daban daban don raya dangantakar dake tsakaninsu da samar da gudummawa wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China