Shugaba Xi ya jaddada cewa, kawancen kasashen Larabawa ya dukufa ka'in da na'in wajen shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya, da bada shawarar daidaita matsaloli ta hanyar siyasa, tare kuma da yin kokarin hada kan kasashen Larabawa, wannan babban abun yabawa ne. A watan Yulin bara, an yi taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da kasashen Larabawa a birnin Beijing, inda bangarorin biyu suka amince da kafa wata huldar abota bisa manyan tsare-tsar tare da yin hadin-gwiwa da neman ci gaba kafada da kafada, al'amarin da ya kasance sabon mafari na hadin-gwiwar Sin da kasashen Larabawa. Xi ya kara da cewa, Sin tana fatan yin kokari tare da kasashen Larabawa don kara samun fahimtar juna, da inganta hadin-gwiwa da mu'amalar al'adu, da tabbatar da aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", don kara kyautata dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da kasashen Larabawa, tare kuma da bada gudummawa ga raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya.(Murtala Zhang)