Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya bukaci hukumomin kula da harkokin jama'a, da su mayar da hankali kan aikin yaki da fatara, kungiyoyin musamman da batutuwan da suka shafi jama'a, ta yadda za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban askawarar kasar, ya bayyana hakan ne, cikin wani umarni da aka karanta a taron harkokin jama'a na kasa da aka gudanar yau Talata a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.(Ibrahim)




