in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya gana da tawagar majalissar dattawa
2019-04-02 09:25:54 cri

Shugaba Xi Jinping ya gana da tawagar majalissar dattawa mai kunshe da wasu tsofaffin shugabannin kasashe a jiya Litinin, a babban zauren taruwar Jama'a dake nan birnin Beijing.

Tsohon shugaban kasar Ireland Mary Robinson ne ya jagoranci tawagar. Sauran dattawan dake cikin majalissar sun hada da tsohon babban magatakardar MDD kuma shugaban dandalin Boao Ban Ki-moon, da kuma tsohon shugaban kasar Mexico Ernesto Zedillo wanda ya yi tsokaci a madadin dattawan.

Cikin jawabinsa ga tawagar, shugaba Xi ya ce kasar Sin wata muhimmiya kasa ce kawai cikin kasashe masu tasowa, amma ba ta taba watsi da nauyin dake wuyanta game da sha'anin kasa da kasa ba.

Shugaban ya ce, Sin na fatan gudanar da hadin gwiwa, domin cimma nasara tare, da kuma taimakawa ci gaban kasashe masu tasowa. Ya ce shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, shawara ce da za ta amfani dukkanin sassa karkashin tsari na hadin gwiwa.

A nasu bangare, dattawan sun taya kasar Sin murnar cika shekaru 70 da kafa sabuwar jamhuriyar al'ummar kasar Sin, da kuma ci gaban da kasar ta samu ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa, baya ga irin rawar da kasar ta taka wajen ingiza harkokin cudanya tsakanin sassa daban daban, duk kuwa da kalubalen da sashen ke fuskanta.

Dattawan sun kara da cewa, har kullum Sin na nacewa manufofi da ka'idojin MDD, tana kuma ba da gudummawa a ayyukan wanzar da zaman lafiya da ci gaban nahiyar Afirka.

Tsohon shugaban Afirka ta kudu marigayi Nelson Mandela ne ya kafa majalissar dattawan a shekarar 2007, domin bayar da tallafi wajen warware tashe-tashen hankula ta hanyar tattaunawa, tare da zakulo hanyoyin shawo kan matsalolin dake addabar duniya, kamar fatara da kuma cututtuka. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China