Shugaba Xi ya ce shigar kowa da kowa wannan muhimmin aiki, zai ingiza manufar shuke dazuka, wadda za ta samar da sakamakon da ake fata.
Shugaban na Sin wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar, ya yi wannan kira ne a Litinin din nan, yayin wani gangami na shuka itatuwa da ya gudana a nan birnin Beijing. (Saminu Hassan)




