in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsawon rayuwa a Nijeriya ya ragu zuwa shekaru 52
2019-04-03 09:51:12 cri
Wata sabuwar kididdiga ta hukumar NPC mai kula da yawan al'umma ta Nijeriya; kasa mafi yawan al'umma, ta ce tsawon rayuwar al'ummar kasar, ya ragu zuwa shekaru 52.2.

Cikin wata sanarwa da ta fitar jiya a Abuja babban birnin kasar, hukumar NPC ta tabbatar da cewa baki daya tsawon rayuwar al'ummar kasar ya ragu da shekaru 3.

Kididdigar hukumar lafiya ta duniya WHO ta 2018, ta ce tsawon rayuwa a Nijeriya zai tsaya kan shekaru 55.2, inda kasar ta kasance ta 178 a jerin kasashen duniya a wannan fanni.

Tsawon rayuwar na nufin matsakaicin adadin shekaru da ake sa ran jariri zai rayu idan aka ci gaba da mutuwa kamar yadda ake yi yanzu.

Hukumar NPC ta ce mutanen dake da shekaru 60 sama, basu wuce kaso 5 cikin jimilar adadin al'ummar kasar ba. Ta ce an yi kiyasin jimilar al'ummar kasar a yanzu, ta kai sama da miliyan 198 inda a kowacce shekara ake samun karuwar adadin da kaso 3.2.

Sannan yuwar haihuwar kowacce mace na kan kaso 5.5. kuma kaso 63 na al'ummar kasar su ne 'yan kasa da shekaru 25, sannan, 'yan kasa da shekaru 15 su suka mamaye kaso 42 na al'ummar kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China