in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya zai yiwa 'yan kasar bayani game da batun Albashi Mafi Karanci
2019-04-04 19:52:51 cri

Labarin da shafin jaridar Leadership A Yau ta wallafa, na cewa Fadar shugaban kasar Najeriya ta bayyana dalilan da ya sa har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari bai sanya hannu a kan dokar mafi karancin albashi ba wanda tuni majalisar wakilai da ta dattawa suka sanya hannu suka kuma mikawa shugaban kasar domin tabbatar da shi a matsayin doka.

A ranar 19 ga watan Maris din nan ne, majalisar Dattawa suka amince da a biya naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi a kasar. Majalisar Dattawa ta bi sahun takwarorinsu na majalisar wakilai bisa amincewa da naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi.

A makon da ya gabata ne dai, aka yika watsa labarai a shafukan sada zumunta cewa; shugaban kasar ya sanya hannu kan dokar albashi mafi karancin. Sai dai a yayin da yake zantawa da Jaridar The PUNCH a Abuja a jiya Laraba, mai taimakawa shugaban kasar akan harkokin majalisar Dattawa, Sanata Ita Enang, ya ce shugaba Buhari har yanzu bai sa hannu kan dokar ba, saboda yana nazarin dokar tare da bin wadansu ka'idoji kafin ya sanya hannu. Kuma, nan ba da jimawa ba zai yiwa 'yan kasa bayani akan matsayarsa dangane da dokar. Ya ce, amma batun cewa shugaban kasa ya sanya hannu kan dokar, wannan sam ba gaskiya ba ne.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China