in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin saman Nijeriya ta dakile yukurin wasu hare-hare tare da kashe 'yan bindiga 5 a yankin arewa maso yammacin kasar
2019-04-02 09:39:19 cri
Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce dakarunta na musammam, sun kashe 'yan bindiga a kalla 5 yayin dakile wasu hare-hare a kauyuka 2 na jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar.

Kakakin rundunar Ibikunke Daramola, wanda ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya ce a ranar Lahadi ne 'yan bindigan suka farwa kauyukan Hayin Mahe da Hayin Kanawa dake Gusau, babban birnin jihar, inda ya ce da yawa daga cikin maharan sun tsere cikin daji da raunukan harbi.

Ibikunle Daramola, ya ce yayin harin, an sace wasu mazauna kauyukan, ciki har da mata 2 da yaro guda. Sai dai kuma jami'an da suka bi sawun maharan da suka tsere, sun yi nasarar ceto mutanen bayan sun yi bata kashi da su.

A cewarsa, daukin gaggawa da jami'an sun ka kai ya biyo bayan bayannan sirrin da suka samu game da ayyukan wasu 'yan bindiga a yankin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China