in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutane 1,000 ne suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
2019-04-06 15:41:09 cri

MDD ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya karu a wannan mako, inda ya zarce 1,000.

A cewar kakakin MDD Stephane Dujarric, hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce an samu karuwar adadin ne a wannan makon, tana mai bayyana matsalolin muhalli da wasu dimbin kalubale da ayyukan dakile yaduwar cutar ke fuskanta.

Yayin taron manema labarai da aka saba yi, Stephane Dujarrice ya ce, an tabbatar da mutane 1,041 sun kamu da cutar, ciki har da 629 da suka mutu. Inda kuma aka sallami mutane 338 da suka yi jinya a cibiyoyin kula da masu cutar, bayan sun kamu da ita.

Ya ce WHO dake aiki karkashin gwamnatin kasar da hadin gwiwar sauran hukumomi, ta ce jami'ai na aiki domin samun amincewa daga al'ummomi da kara kai dauki a yankunan.

Kakakin na MDD ya kara da cewa, hukumar lafiyar ta ce sabuwar dabararta ta kara shigar da al'ummomin da abun ya shafa cikin ayyukanta ya fara haifar da kyawawan sakamako. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China