in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta bayyana fatan kawo karshen annobar cutar Ebola a Kongo Kinshasa cikin watanni 6
2019-03-15 10:33:58 cri
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, yanzu an samu sassauci game da annobar cutar Ebola a kasar Kongo Kinshasa, hukumarsa na fatan za a kawo karshen annobar a cikin watanni shida masu zuwa. A hannu guda kuma, ya ce, duk da harin da wasu dakaru masu dauke da makamai suka kai hari kan wasu cibiyoyin ringakafi da shawo kan cutar Ebola, hukumar WHO ba za ta janye daga kasar ba.

Babban daraktan ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a jiya Alhamis a Geneva, yana mai cewa, a watan Agustan bara ne, cutar ta barke karo na 10 a tarihin kasar ta Kongo Kinshasa. Yanzu haka hukumar WHO da abokan huldarta na tafiyar da wasu cibiyoyin yin rigakafi da shawo kan cutar a yankunan dake fama da cutar domin taimakawa kasar kawar da wannan cuta. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China