in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda tana horas da jami'an lafiyarta dabarun yaki da cutar Ebola
2019-01-09 09:40:09 cri

A jiya ne ma'aikatar lafiya ta kasar Rwanda ta kaddamar da wani shiri na kara zaburar da jami'an lafiya da sauran masu ruwa da tsaki dabarun hana barkewa da sa-ido ko da cutar za a samu barkewar cutar a kasar.

Shirin na kwanaki hudu, wanda aka bude a jiya har zuwa 11 ga wannan wata, an fara shi ne a gundumar Rusizi dake yammacin kasar wadda ke iyaka da Jamhuriyar demokiradiyar Congo.

Manufar shirin samun horon dai ita ce, nazartar yadda jami'an lafiya a matakai daban-daban, da masu aiki a dakunan bincike da ma shugabannin al'umma za su tunkari cutar idan aka samu rahoton barkewarta.

Yayin shirin samun horon, an yi gwajin yadda za a kula da wadanda cutar ta kama, da yadda za a ba su magani da ma yadda za a binne gawarsu ko da cutar ta yi ajalinsu.

Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce, ko da yake a halin yanzu ba a samu rahoton wanda ake zato ko aka tabbatar ya kamu da cutar a kasar ba, duk da haka za ta ci gaba da ganin jami'an lafiyarta gami da sauran masu ruwa da tsaki na cikin shiri, ta hanyar shirya musu shirin horaswa game da dabarun kandagarki da ma hana yaduwar cutar.

Tun lokacin da cutar ta barke a Jamhuriyar demokiradiyar Congo, kasar Rwandan ta tsaurara matakan kandagarkin hana yaduwar cutar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China