Har yanzu, Katwa da Butembo dake arewa maso gabashin kasar, su ne yankunan da aka fi damuwa da su, yayin da ake samun karuwar a wuraren da babu yawan jama'a.
A cikin makonni 3 da suka gabata, an samu mutane 79 da suka kamu da cutar daga yankuna 40 dake cikin shiyoyin 12, sai dai babu sabon rahoton wani da ya kamu da cutar a Beni, daya daga cikin inda cutar ta fara barkewa. WHO na ganin wannan a matsayin ci gaba, la'akari da karfin barkewar cutar a yankin. (Fa'iza Mustapha)