in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barkewar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ita ce mafi girma na biyu tun bayan da cutar ta barke a yammacin Afrika
2019-01-31 11:00:12 cri

MDD ta ce barkewar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ita ce mafi girma na biyu a tarihi, tun bayan barkewar cutar a yammacin Afrika cikin shekarar 2014 zuwa 2016.

A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, barkewar cutar ta yi sanadin mutuwar mutane 461 daga cikin mutane 689 da tabbatar sun kamu da ita da kuma 54 da aka kyautata zaton sun kamu.

An samu barkewar cutar ta farko a Yammacin Afrika ne a kasar Guinea, cikin watan Disamban 2013. Daga can ne cutar ta yadu zuwa kasashe makwabta wato Liberia da Saliyo, daga nan kuma ta wuce zuwa Italiya da Mali da Nijeriya da Senegal da Birtaniya da kuma Amurka.

WHO ta ce annobar ta kare ne a watan Yunin 2016, inda jimilar mutane 28,616 suka kamu, ciki har da 11,310 da suka mutu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China