Sakataren yada labarai na kasar Nick Mangwana, wanda ya wallafa batun a shafinsa na Tweeter a jiya Lahadi, ya ce Shugaba Mnangagwa wanda a baya ya kai ziyara lardin Manicaland, zai kara ziyartar lardin da sauran yankunan da iftila'in ya shafa a larduna 3 na Mashonaland ta gabas da Masvingo da kuma Midlands.
Sakataren ya kara da cewa, abu ne mai kyau shugabanni su shiga cikin al'umma su kuma nazarci abubuwa da kansu.
Shirin tattauna batutuwan kasar ya kunshi 'yan takarar shugaban kasa na zaben 2018 da wasu daga cikin jami'an wasu jam'iyyun.
Emmerson Mnangagwa, shi ne wakilin Jam'iyyar ZANU PF mai mulki, sai dai babbar jam'iyyar adawa ta MDC dake karkashin Nelson Chamisa, ta yi watsi da shirin, tana mai zargin cewa shugaba Mnangagwa ba shi da gaskiya. (Fa'iza Mustapha)