Da yake karin haske game da rahoton, yayin wani gangami na bikin ranar kasa da kasa ta wayar da kai, da inganta ayyukan kau da ababen fashewa da aka gudanar a birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno, babban jami'in tsare tsare na hukumar ta UNMAS Lionel Pechera, ya ce ababen fashewa da ake bunnewa na zama wani babban kalubale ga manoma, wanda kuma hakan ke kara ta'azzara yanayin karancin abinci a sassan arewa maso gabashin Najeriya.
Jami'in ya kara da cewa, wasu daga sansanonin tsugunar da 'yan gudun hijira na cikin wurare dake dauke da irin wadannan ababen fashewa da ake bunnewa, wadanda a lokuta da dama ke raunata, ko ma hallaka fararen hula.
Lionel Pechera ya kara da cewa, wayar da kan al'umma, da tallafawa wajen aikin kawar da irin wadannan ababen fashewa daga maboyar su, muhimmin mataki ne na kare rayuka da dukiyoyin al'umma, tare kuma da samar da dama ta komawar al'ummun da suka tserewa gidajen su zuwa yankunan su.(Saminu Alhassan)