Dakarun tsaron hadin gwiwar, a yayin da suke gudanar da ayyukansu, sun gano wasu tarin makamai a wani waje dake tafkin Chadi, Timothy Antigha, jami'in rundunar sojojin Najeriya wanda kuma shine babban jami'i mai magana da yawun rundunar tsaron hadin gwiwar ya bayyana hakan.
An kaddamar da aikin farautar mayakan 'yan ta'addan ne a yankin Tumbun Rego, wanda shine babbar maboyar mayakan 'yan ta'addan dake tafkin Chadi, inji Antigha
Tumbun Rego, wani sanannen tsibiri ne a tafkin Chadi, wanda aka yi amannan shine wajen da manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram ke samun mafaka.
An gano gawarwakin mayakan 'yan ta'addan 33 a yankin Tumbun Rego, yayin da ragowar 22 aka hallakasu a wani harin na daban wanda dakarun hadin gwiwa suka kaddamar a yankin Arege dake kan iyakar Najeriya, wanda shima wata babbar maboya ce ta mayakan Boko Haram dake kusa da tafkin Chadi.