in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta kashe fararen hula 14 tare da sace wasu mata a Niger
2019-03-26 10:12:42 cri

Fararen hula a kalla 14 ne aka kashe tare da sace wasu mata 2, ranar Asabar da daddare, a wani jerin hare-hare da kungiyar Boko Haram ta kai wasu kauyuka 3 na yankin Gueskerou dake shiyyar Diffa na kudu maso gabashin Niger, kusa da iyakar kasar da Nijeriya.

An tabbatar da aukuwar hare-haren ne a shafin sada zumunta na sabon gwamnan shiyyar Diffa, Mohammed Mouddour, wanda ya je yankin domin ganin illar da hare-haren suka haifar, da kuma mika jajen gwamnatin kasar ga wadanda al'amarin ya shafa.

Gwamnan ya ce, 'yan kungiyar ta'adda na amfani ne da janyewar kogin Yobe wajen dawowa da kai hare-hare a baya bayan, inda suke tsallakawa daga iyakar Nijeriya su kai hari kan fararen hula.

Gwamnan ya sanar da cewa, an dauki muhimman matakan kare aukuwar irin wadannan hare-hare ta hanyar tura jami'an tsaro yankunan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China