in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Sama da mutane 60 sun mutu yayin da dubbai suka tsere sanadin rikici a Nijeriya
2019-01-31 10:16:15 cri

Sama da fararen hula 60 ne suka mutu, yayin da dubbai suka tserewa gidanjensu, sanadiyyar hare-hare akai-akai da kungiyar Boko Haram ke kai yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Yayin taron manema labarai da aka saba yi, kakakin Sakatare Janar na MDD Stephane Dujarric, ya ce fararen hula 60 zuwa 100 ne aka kashe yayin harin baya-bayan nan da aka kai a farkon wannan makon.

Ofishin dake kula da harkokin jin kai na MDD, ya ce mutane 30,000 sun tsere daga garinsu na Rann, dake arewa maso gabashin kasar, zuwa Kamaru, inda wasu dubbai ke neman mafaka a yankunan Ngala da Maiduguri, biyo bayan hare-haren Boko Haram.

A cewar Stephane Dujarric, kungiyoyin agaji abokan huldar MDD sun kaddamar da aikin agaji na gaggawa tare da nazarin bukatun da ake da su a Ngala. Jami'an agajin ba sa iya zuwa garin Rann tun bayan harin da aka kai a tsakiyar watan Janairu.

A Kamaru kuwa, shirin samar da Abinci na duniya WFP, ya ce yana shirin rabon abinci ga 'yan gudun hijira 13,500, yayin da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta duniya UNHCR, ke shirin samar musu matsuguni da sauran tallafi cikin kwanaki masu zuwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China