in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun kashe sama da mayakan Boko Haram 100
2019-01-08 09:29:42 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe sama da mayakan Boko Haram 100 tare da gano wasu makamai da albarusai a wani farmaki na baya-bayan nan da suka kaddamar da nufin kawar da gyauron 'yan kungiyar a yankin arewa maso gabashin kasar.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, mai magana da yawun rundunar sojojin kasar, Sani Kukasheka Usman, ya bayyana vewa, sojojin sun kashe mayakan na Boko Haram ne yayin wani samame da suka kaddamar a jihohin Yabo da Borno dake yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Sai dai sanarwar ba ta yi wani karin haske game da yawan 'yan ta'addan da aka kashe da ma lokacin da sojojin suka kaddamar da samamen ba.

Wasu bayanai na cewa, sojojin sun kaddamar da samame kan mayakan Boko Haram wadanda ke kokarin kafa daular musulunci a shiyyar arewa maso gabashin kasar tun a shekarar 2009 ne a yankunan Goniri, Damasak, Kross Kauwa, da Monguno dake fama da tashin hankali da dai sauransu.

A halin da ake ciki kuma, sojojin sama na kasar, sun yi nasarar lalata motocin dake dauke da bindigogi da sauran kayayyaki na mayakan, yayin da suke taimakawa sojojin kasa ta sama da ma kokarin kama 'yan ta'addan da suke kokarin tserewa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China