Aikin gina kamfanin wanda ya lashe dala miliyan 350, dake yankin Kalambaina a jihar Sokoto a arewa maso yammacin kasar, ya kasance wata babbar cibiyar fitar da siminti zuwa kasashen ketare a shiyyar, wanda kamfanin Sinoma na kasar Sin ya gina.
Kamfanin zai iya samar da adadin siminti metric ton miliyan 1.5 a duk shekara, kana zai samar da ayyukan yi na kai tsaye kimanin 2,000 da kuma wasu ayyukan na wucin gadi kimanin 10,000 a fadin kasar.
Mataimakin shugaban kasar ya bukaci rukunin kamfanonin na BUA da su hada kai da sauran kamfanonin siminti don rage farashin simintin a kasar.
Kaddamar da kamfanin simintin ba wai nasara ce ga rukumin kamfanonin BUA kadai ba, har ma ga kamfanin simintin da tattalin arzikin Najeriya, in ji Osinbajo.
Ya ce nan da wasu 'yan shekaru masu zuwa kasar za ta samu gagarumin cigaba ta fuskar bunkasuwar kayayyakin more rayuwa. (Ahmad)