in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bada tallafin aikin gina filin saukar jiragen saman Najeriya a yanki mai arzikin mai
2018-10-26 10:10:56 cri

A jiya Alhamis shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon aikin filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Fatakwal wanda kasar Sin ta bada tallafi wajen gina shi da nufin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Aikin gina filin sauka da tashin jiragen saman na Fatakwal, ya lashe dalar Amurka miliyan 600, a jihar Rivers mai arzikin mai dake shiyyar kudancin kasar, ana sa ran aikin zai samar da ingantattun titunan sauka da tashin jiragen saman, wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da cigaban kayayyakin more rayuwar jama'a a Najeriyar.

Da yake jawabi a lokacin kaddamar da sabon aikin filin jirgin saman, Shugaba Buhari ya bayyana ingancin kayayyakin aikin wanda darajarsu ta kai matsayi na kasa da kasa, ya kasance wani muhimmin cigaba ne ga masu zirga zirga na kasa da kasa a Najeriyar, wadda kasa ce mafi yawan al'umma a fadin Afrika.

Shugaba Buhari ya ce, aikin ya zo a daidai lokacin da Najeriyar ke bukatarsa. 'Gwannatin tarayya ta amsa kira a bangaren sufurin jiragen sama wanda a halin yanzu bangaren ya zama wani muhimmin ginshiki na bunkasa cigaban tattalin arziki, a sakamakon yadda ake samun karuwar masu sha'awar yin tafiye-tafiye, da sarar kayayyaki, da harkokin yau da kullum ta hanya mafi tsaro da kwanciyar hankali." In ji shugaban kasar.

Sabon ginin wanda ke da hawa biyu, ya hada da wajen saukar kananan jirage, da kuma wajen saukar manyan jiragen dakon kaya, da wajen gudanar da sauran kananan ayyuka.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China