in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
First Bank: Zai yayata yarjejeniyar musayar kudade tsakanin Sin da Najeriya
2018-07-24 10:42:22 cri

Babban wakilin bankin nan na First Bank a Najeriya Andy Wang, ya ce bankin zai yi kyakkyawan amfani da yarjejeniyar musayar kudade da kasashen Sin da Najeriya suka kulla wajen yayata alaka da kuma kara bunkasa damammakin harkokin kasuwanci dake tsakanin kasashen biyu.

Jami'in wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya, ya ce bankin na son zama wata gada tsakanin harkokin kasuwancin kasashen Najeriya da Sin ta hanyar yayata yarjejeniyar.

A cewarsa, musayar kudaden za ta taimaka wajen saukaka harkokin cinikayya tsakanin kasashen biyu, ba tare da fuskantar kalubalen neman canjin wasu kudaden ketare ba.

A ranar 27 ga watan Afrilun wannan shekara ce babban bankin Najeriya CBN ya sanya hannu kan yarjejeniyar musayar kudade ta dala biliyan 2.5 da babban bankin al'umma na kasar Sin.

Manufar wannan tsari dai ita ce samar da isassun kudade ga masu masana'antun Najeriya da Sin da kuma taimakawa asusun kudaden ajiyar ketare na kasashen biyu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China