in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar Lagos ta kaddamar da cibiyar nazarin ci gaban Najeriya da Sin
2018-11-08 09:45:56 cri

Jami'ar jihar Lagos dake kudancin Najeriya ko UNILAG a takaice, ta kaddamar da cibiyar nazarin ci gaban dangantakar Najeriya da kasar Sin, domin tallafawa wajen bunkasa alakar bangarorin ta fannoni da dama.

Sabuwar cibiyar da aka kaddamar a harabar jami'ar a ranar Talata, na kunshe da bayanai da za su iya taimakawa Sinawa masu sha'awar zuba jari a Najeriya, da ma 'yan Najeriyar dake da burin shiga kasuwannin Sin, ta yadda za su yi hadin gwiwa da juna da cimma moriya tare.

Da yake tsokaci game da tasirin da wannan cibiya za ta yi, mataimakin shugaban jami'ar Oluwatoyin Ogundipe, ya ce cibiyar za ta bunkasa harkokin ilimi, da raya musayar al'adu tsakanin Sin da Najeriya. Kuma a cewar sa, an kafa ta ne domin baiwa jami'ar damar shiga tsarin ci gaba na raya ilimi a matakin kasa da kasa.

Mr. Ogundipe ya kara da cewa, cibiyar za ta kuma samar da damar nazartar tarihi, da ci gaban kasar Sin, da na Najeriya, da samar da damar cudanya tsakanin al'ummun sassan biyu, ta yadda za su zakulo sassan da kasashen su ke da karfi da kuma rauni, dukka dai da nufin zaburar da matakan samar da ci gaban da ake fata.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China