in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sace wani limamin darikar Katolika a Nijeriya
2019-03-27 10:13:56 cri
Rundunar 'yan sandan Nijeriya, ta ce wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun sace wani limamin darikar Katolika a kauyen Ankuwa na yankin Kachia mai fama da riginginmu, dake jihar Kaduna na yankin arewacin kasar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Yakubu Sabo, wanda ya bayyana haka ga manema labarai, ya ce tuni jami'an tsaro suka fara bincike a kauyen da nufin ceto limamin mai suna John Bako Shekwolo da kuma cafke wadanda suka sace shi.

Yakubu Sabo ya ce an sace John Shekwolo ne ranar Litinin da da daddare. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China