Manazartan harkokin tattalin arziki sun bayyana cewa, yawan asusun ajiyar kudaden waje da babban bankin Najeriya ke dashi ya karu har na tsawon makonni uku, kana adadin asusun ajiyar kudaden wajen ya karu da dala biliyan 1.8 ko fiye a wata daya da ya gabata.
Duba da raguwar man fetur da kungiyar OPEC ke samarwa, da takunkumin da Amurka ta kakabawa Venezuela da Iran, farashin gurbataccen man fetur ya karu a shekarar da muke ciki, kuma an yi hasashen cewa, darajar kudin Najeriya wato Naira ba zata ragu ba a cikin matsakaici da gajeren zango. (Murtala Zhang)