Cikin wata sanarwar da ta aikewa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Litinin, kungiyar Norwegian Refugee Council (NRC) ta bukaci a dauki matakan dakile barazanar da yankin na arewa maso gabashin Najeriya ke fuskanta, yankin dake karbar bakuncin dubban mutane wadanda suka kauracewa gidajensu a sakamakon yawan hare-haren mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram.
A cewar wani rahoton cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya, a shekarar 2018, an samu rahoton mutane 50,719 daga jihohin kasar 30 da ake zaton sun kamu da cutar ta kwarala.
NRC ta yi gargadin cewa, mai yiwuwa ne a samu saurin bazuwar cutar a wannan shekarar kasancewar ana samun karuwar mutane dake kauracewa gidajensu lamarin da ke haifar da cunkoson jama'a a sansanonin. (Ahmad Fagam)