in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sashen ba da hidimar manhajojin kwamfuta na Sin ya samu ci gaba a shekarar bara
2019-02-06 15:51:52 cri

Sashen samarwa da ba da hidimar manhajojin kwamfuta da na fasahar sadarwa na Sin, ya samu ci gaba a shekarar bara, inda ya samar da karin haraji da riba mai tarin yawa.

Wata majiyar ma'aikatar raya masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa. An ce a shekarar ta bara, kudaden shiga da sashen ya samar ya kai kudin Sin Yuan triliyan 6.31, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 940, adadin da ya karu da kaso 14.2 bisa dari idan an kwatanta da na shekarar 2017.

Kaza lika tsantsar riba da aka samu a fannin ta karu da kusan kaso 9.7 bisa dari a shekarar, wanda adadin ta ya kai Yuan biliyan 807.9. Majiyar ma'aikatar raya masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta ce, sashen samarwa da ba da hidimar manhajojin kwamfuta da na fasahar sadarwa ta Sin na samun madaidaicin ci gaba, ya kuma zamo jigon raya tattalin arziki a fannin amfani da na'urorin fasahar sadarwa, matakin da ya haifar da kara zaburar da bunkasar masana'antu, da sauran sassan ci gaban kasa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China